An kirayi gwamnatin jahar Adamawa da ta taimakawa manoma.....AbdulRazak
An kirayi gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da tayi dukkanin abunda suka dace domin taimakawa manoma dake fadin jahar baki daya.
Sarkin noman yakkire Sakin ruwan Gerio Alhaji AbdulRazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola.
Alhaji AbdulRazak Abubakar ya yabawa gwamna Fintiri bisa na mijin kokari da yakeyi wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar harma da kokarin da yakeyi wajen tallafawa manoma dake fadin jahar.
Alhaji AbdulRazak ya shawarci gwamnan dacewa in za a tallafawa manoma abi ta sarakunan gargajiya wato irin su masu angwani jimilloli hakimai Wanda acewarsa hakan zai taimaka domin sune sukasan asalin manoma dake yankunansu.
AbdulRazak ya kuma baiyana cewa manoma suna taka rawan gani wajen bunkasa tattalin arziki dama rage rashin aikinyi musammanma a tsakanin matasa dake fadin jahar.
Don haka akwai bukatan a maida hankali wajen taimakawa manoma akan lokaci musammanma a wannan lokaci na damina da Kuma irin hali da ake ciki na matsalar rayuwa.
Alhaji Abubakar ya kirayi Al umma musammanma wadanda ba manoba da suyiwa Allah da Manzonsa da su bari a baiwa ainihin manoma kayakin noman domin baiwa manoma damar wadatar da wadaceccen abinci.
A cewar AbdulRazak dai yanzu haka manoma na cikin halin ha ula I saboda haka ya kamata a taimaka musu domin Suma su samu saukin gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
SANARWA. SANARWA. SANARWA.
Hukumar makaramtar NA IBI ACADAMY dake Damsawa a cikin garin Jimeta dake karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa. Tana garin cikin sanar da Al umma cewa ta fara sayar da Form din shiga makaramtar daga matakin Firamaer da sauransu. Kuma makarantar ta shahara wajen karantar da bangarori da dama da su hada na addini dama na zamani. Kamar haka.
A bangaren addini ana karantar da haddan Al ku ani Maigirma, Nahaw, Tauhid, Luggatul Arabiya, da dai sauransu.
A bangaren Boko kuwa makarantar na karantar da darasin lissafi wata Maths da harshen turanci English, Computer, Social Study, Agriculture, da dai Sauransu.
Ana zuwa makarantar cikin kwanaki biyar wato daga litinin zuwa Jumma a Kuma ana fara karantarwane daga karfe bakwai na safe zuwa karfe hudu da rabi na yamma a kowace tana. Bugu da Kari makarantar na ciyar dalube abinci sau daya a rana sannan akwai motocin debo dalube da Kuma mayar dasu gidajensu kana akwai masu kula da dawainiyar dalube a cikin makarantar ta NA IBI ACADEMY .
Domin karin bayani ko sayan Form din sai a ziyarci harabar makarantar dake dake Damsawo ko a tuntubi Number wayoyin waya kamar haka. 07063516642.
08024772558.
Sai kunzo
Comments
Post a Comment