AN SHAWARCI AL UMMA MISULMAI DA SU SANYAWA YARANSU SON MANZON ALLAH TUN SUNA YARA DOMIN CIGABAN ADDININ MUSULUNCI.
Daga Alhassan Haladu Yola. An shawarci iyaye musammanma mata da sukasance masu koyawa yaransu son manzon Allah da iyalensa tun suna Yara domin hakan zai taimaka wajen inganta rayuwarsu yadda ya Kamata. Hajiya Amina Muhammed Bashir ne ta Bada wannan shawara a lokacin da take jawabi a wurin bikin Maulidi Manzon Allah da aka gudanar a gidan Modibbo Ahmadu Ganye dake cikin karamar Hukumar Ganye a jahar Adamawa. Hajiya Amina tace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace ku koyawa yaranku abubuwa uku Son Allah, son Annabi, da iyalen gidansa don haka ya Kamata iyaye su Kara himma wajen nunawa yaransu son Annabi da Kuma Yi masa biyayya. Ta Kuma kirayi wadanda suka halarci bikin na maulidi da sukasance suna amfani da abinda sukaji ma nasihohi da aka gudanar a waurin bikin. Domin Samun cigaba addinin musulunci yadda ya Kamata. Ta Kuma shawarci mahalarta bikin da sukasance jakatu wajen isar da duk bayanai da sukaji ga sauran Al umma da Basu Samu damar hakartar bikin maulidi b...