An bukaci da maida hankali wajen baiwa yaran mata Ilimi.

An shawarci iyaye da sukasance masu Kai yaransu musammanma mata makarantu domin su samu ilimin addinin dana zamani domin Suma su samu damar karantar da iyalensu dama tarbiyar yaransu yadda ya kamata. Hajiya Maryam Babalau Hassan ce tayi wannan kira a zantawarta da manema labarai a Yola. Hajiya Maryam Babalau yace baiwa yaran mata ilimi Yana da mutukan muhimmanci domin itace farkon makarantar yara, Kuma da zaran an karantar da mace Daya to tamkar an karantar da Al ummane. Saboda haka Yana da kyau a maida hankali wajen karantar da ya mace. Hajiya Maryam da Kuma kiarayi yaran matam da suma su zage damtse wajen Neman ilimi na addini Dana zamani domin inganta rayuwarsu yadda ya kamata. Maryam ta Kuma kirayi masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da Suma su bada tasu gudumawa r wajen baiwa yaran matam ilimi Mai nagarta a Koda yaushe.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT