An baiyana cewa Al umma sukasance masu sanya tsoron a dukkanin aiyukansu.
A yayinda aka fuskanci Azumin watan Ramadan an kirayi Al ummàh musulmai da sakasance masu sanya tsaron Allah madaukakin sarki a dukkanin aiyukansu a lokacin Azumin watan Ramadan domin samun taimakon Allah a Koda yaushe.
Malama Aisha Khamis ce tayi wannan kira a lokacin taron Ramadan lecca Wanda kungiyar mata musulmai ya tarayya FOMWAN Shiyar jahar Adamawa ta shirya a yola.
Malama Aisha Khamis ta Kuma shawarci Al ummah musulmai da a Koda yaushe sukasance masu taimakawa marassa galihu wadanda ke cikin Al umma musulmai musammanma a lokacin watan Ramadan.
Ta Kuma kirayi musulmai da suyi amfani da watan Ramadan wajen yiwa kasa adu o I dama shuwagabanin domin su samu damar dakile dukkanin kalubale da kasan nan ke fuskanta.
Da yake gabatar da nashi lekca shugaban makarantar higher Islamic ta FOMWAN Ustas Sa Idu Andulhamid yace watan Ramadan wata ne da yake da mutukan muhimmanci ga Al umma musulmai saboda haka ya shawarci Al umma musulmai da su rubaiya ibadansu da bada sadaka a lokacin Azumin watan Ramadan.
Ya Kuma kirayi shuwagabanni da sukasance masu la akari da marassa galihu domin su samu saukin rayuwa da Kuma rage radadin wahalar da ake ciki a halin yanzu.
Shima ya shawarci Al umma musulamai da sucigaba da yin adu o I Samar da zaman lafiya a jahar dama kasa baki Daya.
Tunda farko anata jawabi Amiran FOMWAN a jahar Adamawa Hajiya Khadija Buba ta kirayi wadanda suka halarci taron da suyi amfani da abinda sukaji domin samun lada da Kuma hadin Kai a tsakanin Al ummah.
Comments
Post a Comment