An koyawa mata da suka warke daga cutara yoyon fitsari 50 sana o I daban daban a jahar Jigawa.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
Gwamnatin jahar Jigawa tare da hadin gwiwar Gidauniyar Fistula a Najeriya FFN da Kuma Asusun Al umma na majalisar Dinkin duniya wato UNFPA sun horar da mata da suka warke daga cutara yoyon fitsari VVF da yawansu ya Kai hamsin a fadin jahar.
Darectan Gidauniyar Fistula a Najeriya Dr Musa Isa ne ya baiyana haka alokacinda yake jawabi a wurin bikin yaye mata 50 bayan an koyar dasu sana o l daban daban kauta a Jahun dake jahar ta Jigawa.
Dr Musa Isa ya zanyano irin aiyukan da sukayiwa mata da suka hada da fidar cutar yoyon fitsari da basu magunguna harma da koya musu sana ar dogaro da Kai da Kuma basu kayakin sana o in.
Dr Musa yace watanin hudu sukayi suna horar da matan da suka warke daga cutara da VVF cikin Sana o I da aka koyo musu sun hada da tela, kiwon awaki, dayin maingyada, da dai sauransu.
Ya Kuma kirayi wadanda suka amfana da Shirin da su zama jakadun Gidauniyar ta Fistula wajen wayarwa mata Kai dangane da matsalar tsawon na kuda da Kuma muhimmancin zuwa gwaji a asibitin.
Ya Kuma ambato cewa akwai doka Mai tsauri in har na mijin da ya yasaki matarsa saboda ta kamu da cutar yoyon fitsari.
A nata bangaren ma aikatar harkokin mata da walwala a jahar Jigawa ta yabawa Asusun jama a na majalisar Dinkin duniyar UNFPA da gwamnatin jahar bisa goyon baya da suka bayar domin ganin an samu nasaran aikin fida da Kuma koyar da sana o I tare Kuma da maraba da aiyukan cigaba da Gidauniyar Fistula ta kawowa Al ummar dake fadin jahar.
Daya daga cikin Wanda tayi magana a madadin wadanda suka warke daga cutara sun gode tare da yabawa gwamnatin jahar da Gidauniyar Fistula da Kuma UNFPA saboda ceto rayuwarsu da sukayi.
Cutar yoyon fitsari wato VVF a turance tana samo asaline dai a lokacin haifuwa inda ake samun matsala ta wajen Kari da dai sauransu Wanda Kuma hanya Daya na maganceshi shine yin fida.
Comments
Post a Comment