An shawarci masu ruwa da tsaki a jam iyar APC da sukasance masu hada kansu.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
An shawarci Yan jam iyar APC a jahar Adamawa da sukasance masu hada kansu da baiwa shuwagabani goyon baya domin ganin an samu nasaran a zaben shekara ta 2027.
Hon. Patricia Yakubu ce ta bada wannan shawara a lokacin da ta gudanar da ziyara a dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar.
Patricia tace ta gudanar da ziyaran ne domin ganawa da shugabannin mata ma jam iyar APC tundaga matakin anguwanni har zuwa matakin jahar da zummar Samar da hadin Kai a tsakanin Yan jam iyar ta APC.
Ta Kuma baiyana cewa yana da muhimmanci a hada Kai domin ciyar da jam iyar gaba harma tace ta kasance a cikin harkokin jam iyar a mataki jahar ne saboda tanason ganin jam iyar tacigaba yadda ya kamata a fadin jahar.
Saboda hakanema take tunatar da Yan jam iyar da cewa hadin Kai a tsakanin Yan jamiyar shi zaikasu ga samun nasara maidaurewa.
Ta Kuma baiyana jindadinta da farin cikinta dangane da yadda shuwagabanin matan jam iyar suka bata hadin Kai da goyon baya wannan ya nuna cewa matan dake cikin jam iyar ta APC suna da hadin Kai.
Sun kammala ziyaran ne da taimakawa da kayakin kiwon lafiya a Baban asibitin Numan a matsayin jinkai Wanda Kuma abunda jam iyar ta APC ta sanya a gaba kenan.
Saboda haka ta kirayi Yan jam iyar da suyi dukkanin abinda suka dace domin samun cigaban jam iyar yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment