Ranan mata ta duniya an yabawa maza.

 




Daga Sani Yarima Jalingo.

A yayinda ake gudanar da bikin ranan mata ta duniya an yabawa maza bisa rawa da suke takawa wajen inganta rayuwar mata.



Kwamishiniyar muhalli da sauyin yanayi a jahar Taraba Aisha A Barde ce ta baiyana haka a sakonta na bikin ranan mata ta duniya da ta fitar a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba.




Aisha Barde tace maza sun bada muhimmiyar gudumawa wajen taimakawa mata wanda hakan yakaisu ga samun nasara a dukkanin harkokinsu na yau da kullum.



Saboda haka take baiyana godiyarta da jinjinanta ga maza domin ganin mazan sun samu kwarin gwiwar cigaba da taimakawa mata a Koda yaushe. 



Kwamishiniyar ta Kuma godewa gwamna Agbu Kefas bisa irin dama da ya baiwa mata a cikin gwamnatinsa domin Suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban jahar. Don haka nema take shawartar matan da suyi dukkanin abinda zai kawo daga martaban jaha.




Aisha ta yabawa uwar gidan gwamnan jahar ta Taraba Mis Agyan Agbu Kefas bisa yadda take koyawa mata da matasa sana o I daban daban a fadin jahar.




Kwamishiniyar ta kirayi takwaranta wato kwamishiniyar harkokin mata a jahar Taraba Hon. Merry Sijen da tayi dukkanin Mai yiwa domin samarwa mata da matasa aiyukan Yi domin cika muradun gwamna Kefas na gudanar da aiyukan cigaban jaha.




Ta Kuma kirayi mata da sucigaba da yiwa gwamnatin Kefas adu o I da Kuma bashi goyon baya a matsayinsu na iyaye.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT