Rundunan Yan sanda a jahar Adamawa ta lashi takwabin hukunta duk Wanda aka samu dayiwa doka Karan tsaye a lokacin bikin samun yanci.

 






Rundunan yan sandan jahar Adamawa tare da takwarorinta zasu daukai dukkanin mataki da suka dace domin dakile dukkanin masu yin amfani da bikin ranan yanci wajen zanga zanga saboda haka a shirye suke su shiga kafar wando Daya da duk wadanda keyiwa zaman lafiya Jahar barazana.





Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Sanarwan tace rundunan ta tunin da sanya ido tare da tura Jami anta wuwaren taruwar jama a domin ganin ko a kwai Wanda zai karya doka.





Sanarwan ta kirayi Al umma da sukasance masu taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanain da zai taimaka wajen takawa masu yiwa zaman lafiya barazana birki.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.