Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

A kokarinta da kula da walwan Jami an yan sadan rundunan yan sandan a Najeriya ta bigi kirjin cigaba da kula da walwalan Jami an yan sandan a koda yaushe domin kara musu gwiwar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata. Rundunan karkashin shirinta na inshora. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya gabatarwa magadan yan sandan da suka rasa rayukansu a lokacinda suke yiwa kasa aiki. Takardan karban kudi wa iyalen 32 kudin wanda yawansa yakai Milyon 73,357,394,83. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Kwamishinan ya kuma jadda da aniyar rundunan nayin dukkanin abinda suka dace domin sauke nauyin da yake kanta na kula da jin dadin dukkanin Jami an yan sandan harma da wadanda suka sadaukar da kansu wajen gudanar da aiyukansu harma da kare martaban kasan nan. Kwamishinan yan sandan ya yabawa Babban sifeton yan sandan bisa na mijin kokari da yakeyi na kula da walwalan yan sandan wanda hakan zai taimaka wajen gudanar da adalci dama inganta tsaro.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE