CP ADAMAWA YA UMURCI A GAGGAUTA FARA BINCIKE KAN ZARGIN WANI FASHI DA MAKAMI A WANI GIDA DAKE NGURORE, YOLA KUDU
Daga Alhassan Haladu Yola. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Adamawa, CP Dankombo Morris, Psc(+), ya bayar da umarnin da a gaggauta fara bincike kan wani zargin fashi da makami a Wani gida da ake cewa ta faru a gidan wani matashi mai shekaru 25, Akwarakiram Abel, mai aiki da POS, da ke Sabon Pegi a Ngurore, Karamar Hukumar Yola ta Kudu. Kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya Sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Hakan na zuwa ne bayan korafin da iyalan matashin suka kai cewa a safiyar 21 ga Nuwamba, 2025, tsakanin karfe 3:00 na dare zuwa 4:00, wasu da ba a san su ba, dauke da makamai, suka kutsa gidan, suka farmake shi tare da kwace masa kayansa. A cewar rahoton, ‘yan fashin sun yi masa mummunan rauni da adda, abin da har ya kai ga yanke masa hannu. Kwamishinan ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi don cafke wadanda suka aikata laifin tare da tabbatar da an yi adalci ba tare da bata lokaci ba. Rundunar ta kuma...