KUNGIYAR MANOMA ALBASA TA KUDIRI ANIYAR INGANTA NOMA DA SAYAR DA ALABASA A CIKI DA WAJEN NAJERIYA.









Daga Alhassan Haladu Yola.

 Kungiyar manoma da sayar da Albasa a Najeriya tasha Alwashin bunksa harkokin noma Albasa dama sayarwa a ciki da wajen Najeriya.


Babban sakataren kungiyar a Najeriya Ibrahim Goni Dasin ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.


Ibrahim Goni Dasin yace kungiyar ta gudanar da taro tare da Hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya inda suka tattauna batutuwa da dama ciki harda yadda za a rinka fitar da Albasa zuwa kasashen waje domin sayarwa.


A cewarsa hakan ne zai bunkasa harkokin noma dama kasuwancin Albasa aciki da wajen Najeriya, saboda haka akwai bukutar manoma Albasa a Najeriya da sukasance sun Maida hankali wajen noma Albasa.


Ya Kuma shawarci manoma Albasa da suyi rijista da kungiyarsu Wanda hakan zai basu damar bunkasa harkokin noman Albasa, tare da kiasansu da sukasance masu Neman sanin ilimin noman Albasa musammanma a zamunance.



Ya Kuma kirayi gwamnatin tarayya Dana jihohi dama masu ruwa da tsaki da su Maida hankali wajen tallafawa manoma Albasa Wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa noman Albasa a ciki da wajen Najeriya.


Kawo yanzu dai kungiyar manoma da sayar da Albasa a Najeriya tana kokarin Samar da wuraren ajiya ga albasa domin komai dadewa baza ta lalaceba.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

ADAMAWA STATE POLICE COMMAND CELEBRATES WOMEN POLICE @ 70