A yayinda aka fusskanci bukukuwar kirsimeti dana sabuwar shekara hukumar kare haddura a jahar Adamawa ta tura jami anta dari takwas da hamsin domin ganin an kakmala bukukiwar lafiya.

Hukumar kare haddura ta kasa wato FRSC tace ta kimtsa domin bada kariya a lokaci dama bayan bukukuwar kirsimeti dama sabuwar shekara a fadin jahar Adamawa. Kwamandan hukumar a jahar Adamawa Yelwa D Dio ne ya sanar da haka a zantawarsa da mamema labarai a ofishinsa dake yola. Kwamadan Yelwa yace daman an kirkiro hukumar ne domin rage yawaitar haddura da ake samu akan manya da kananan hanyoyi dake fadin kasan nan baki daya. Mr Dio yace kawo yanzu sun tura Jami an hukumar su dari takwas da hamsin a fadin jahar ta Adamawa domin tabbatar da ganin ba a samu hadduraba a lokaci da ma bayan bukukuwar kirsimeti da sabuwar shekara. Kwamandan yace Jami ansu zasu kasance a majami u dama wurin tarukan jama a a wani mataki na kare haddura dama rayukan al ummar. Harwayau kwamandan yace sukanyi amfani da majami u,masallatai, tashoshi harma da kafafen yada labarai domin fadakar da al umma dangane da kula da tuki ababen hawa musammanma akan manyan tituna dake Najeriya. Ya kirayi matuka ababen hawa musammanma na kasuwa wato masu daukan fasinja da su daina daukan kaya fiye da kima da kuma yin amfani da taya mai inganci domin kaucewa hadari. Ya kuma kara da cewa wanna wata na desemba yana daya daga cikin watanni masu hatsari wato emba months saboda irin tafiye tafiye da akeyi a cikin watannin. Don haka ya kamata direbobi sukasance masuyin taka tsantsan a lokacinda suke tuki. San ya shawarci direbobin da su daina daukan waya a lokacinda suke tuki. Kawo yanzu dai hukumar kare haddura a jahar Adamawa ta shirya motocin da zasu gudanar da sintiri a lunguna da sako sako dake fadin jahar ta Adamawa. Kuma yayi amfani da wannan damar wajen kiran daukacin al ummar jahar Adamawa ta su rinka sanar da hukumar da zaran sunga hatsari ya faru domin daukan matakin gaggawa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE