TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.






DAGA Alhassan Haladu Yola.


A yayinda Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro an kirayi Yan Najeriya da sukasance suna baiwa hukumomin tsaro hadin Kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsu na inganta tsaro a fadin Najeriya baki Daya.






Kwammanda Mafarauta na kasa Kuma sarkin yakin mafarautar Adamawa Alhaji Muhammed Adamu ne yayi wannan Kira a zantawarsa da manema labarai a Yola, fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Alhaji Muhammed Adamu yace baiwa hukumomin tsaro hadin Kai Yana da mutukan muhimmanci Wanda acewarsa hakan zai Karawa hukumomin tsaron kwarin gwiwa wajen gudanar da aiyukansu na tsaron kasa.





Muhammed Adamu yace ya Kamata Al ummar Najeriya sukasance suna taimakawa hukumomin tsaro irinsu, rundunan sojoji, Yan sandan, civil defence, Mafarauta da dai sauransu, da wasu bayanai da zai taimaka wajen dakile aikata laifuka a fadin Najeriya.





Ya Kara da cewa ta baiwa hukumomin tsaron goyon bayane za a Samu damar kawar da Bata gari a jahar tsakanin Al umma baki Daya.




Saboda haka Yana da muhimmanci Yan Najeriya sukasance masu baiwa hukumomin tsaro hadin Kai domin ganin an kawo karshen kalubalen tsaro a fadin Najeriya.




Ya Kuma kirayi iyaye da Suma su Bada tasu gudumawan domin a cewarsa suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen takile matsalar tsaro, saboda sune suke da kaso Mafi tsoka ta baiwa Yara tarbiya, saboda haka hakkinsune sun da waye yaransu suke mu amala, da Kuma sanin Ina suke zuwa gudanar da harkokin su.




A cewarsa dai hakan zai taimaka kwarai wajen inganta tarbiyar yaran masu, don haka sukasance masu Maida hankali sosai dangane da tarbiyar yaransu yadda ya Kamata.




A Kuma shawarci daukacin matasan Najeriya da su Bada tasu gudumawar wajen wanzar da zaman lafiya, da Gina kasa harma da cigaban kasa bai Daya.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT