Akalla mata darine zasu amfana da aikin fida na cutar yoyon fitsari a jahar Bauchi.

A kalla mata darin ne wadanda ke dauke da cutar yoyon fitsari ne suka amfana da aikin fida cutar a cibiyar kula da cutar ta yoyon fitsari ta kasa dake Ningi a jahar Bauchi, Hukumar raya yankin arewa masau gabas tare hadin gwiwar kungiyar dàke taimakawa domin yaki da cutar wato VVF ne suka kaddamar dayin jinyawa wadanda ke dauke da cutar yoyon fitsrin kauta a jahar Bauchi wanda kuma za a tadada aikin a yankin na arewa masau gabas baki daya. Da yake kaddamar da fara aikin kwamishinan kiwon lafiyar a jahar Bauchi Dr Sabir Ahmed wanda darektan kiwon lafiya a jahar Bauchi Robeson Yusuf ya wakilta ya godewa hukumar raya arewa masau gabas da takwaranta ta VVF bisa kokarinsu na taimakawa gwamnatin jahar Bauchi domin kula da lafiya al umma jahar. Yace wanna taimako yazo a daidai don kuwa akwai mata dawa wadanda ke dauke da cutar ta yoyon fitsari amman rashin kudi ya hanasu zuwa asibiti domin yi musu jinya. Saboda haka yana ganin mata da dama zasu amfana da wannan taimako a fadin jahar. Ya kuma kirayi wadanda suka sanaran samun jinya da sukasance masu bin shawarwarin da kwararrun likitocin zasu basu domin kare kansu daga kamuwa da cutar tare kuma da ziyartan asibitin akan lokaci. A sakonsa Babban sakataren jinkai a hukamar raya yankin arewa masau gabas wanda shugabar sashin kiwon lafiya a hukumar Dr Batulu Isa Mohammed ta wakilta kididdiga ya nuna cewa akalla mata dubu biyu ne ke fama da cutar ta yoyon fitsari kuma ba yankin arewa masau gabas kadai sukeba harma da wasu sassan kasan nan. Ta kuma shawarci mata da sukasance masu zuwa awu akan lakaci da zaran sun samu juna biyu domin samun kariya daga kamuwa da cutar ta yoyon fitsari. Dr Batulu tace za ayi dukkanin kokarin da ya kamata domin ganin an taimakawa matan musammanma wadanda ke fama da cutar domin suma su samu saukin rayuwa a tsakanin Al ummah. Batulu tace yanzukam matan zasu kubuta daga yanayin da suka samu kansu a cik na matsalar yoyon fitsari, tare da godewa hukumar gudanarwa cibiya kula da cutar ta yoyon fitsari a Ningi dake jahar Bauchi misamanma wadanda ke aikin fidar cutar da ma aikatan jinya bisa na mijin kokarin da suke yi na kula da masu dauke da cutar. Tunda farko a jawabinta na maraba darektan cibiyar kula da cutar ta yoyon fitsari na kasa dake Ningi a jahar Bauchi Dr Halima Mukaddas tace duba da yadda ake samun karuwan wadanda ke kamuwa da cutar a yankin cibiya zatayi iya kokarinta domin ganin an samu saukin matsalar baki daya. A yankin arewa masau gabas ta kuma nuna jin dadinta da farin cikinta dangane da wannan taimako wanda acewarta wannan abune mai muhimmanci.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.