An bukaci da mabiya addinin kirista suyi amfani da lokacin bikin kirsimeti wajen adu oin zaman lafiya.

A yayinda aka fusaknci bikin kirsimeti na wannan shekara an kirayi mabiya addinin kirista da suyi amfanin da wannan lokaci wajen kautata halaka da al umma domin samun cigaban zaman lafiya a fadin kasanan baki daya. Shugaban kungitayar kiristoci a Najeriya CAN shiyar jahar Adamawa Rev. Dami Manza ne yayi wannan kira a lokacinda ya tattauna da jaridar Al Nur a yola. Rev. Dami Manza yace wannan lokaci da bikin kirisimeti damace ga mabiya addinin kirista da su sadaukar da Kansu wajen neman yardàn Allah Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen hadin kan mabiya addinin kirstan dama sauran al ummah baki daya. Rev. Manza ya kuma shawarci mabiya addinin kirista da su maida hankali wajen yin adu oi domin neman taimakaon Allah wajen kawo dukkanin karshen matsalar tsaro a fadin kasan nan baki daya. Ya kuma yi fatan Allah yasa a kammal bukukuwar kirisimeti lafiya dama shiga sabiwar shekara lafiya. Tare kuma da kammala zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsalaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE