An bukaci malamai da su fadada aiyukansu wajen wayarwa matasa kai
An kirayi malamai da su kara fadada wa azuzzukasu zuwa lunguna da sako sako dake fadin jahar Adamawa dama fadakar da matasa dangane da muhimmancin neman ilimin addini dama samar da zaman lafiya a tsakanin al ummah.
Hakimin Gombi Alhaji Usman Ibrahim sarkin fada ne yayi wannan kira a lokacinda majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa ta shirya taron Da awa a karamar hukumar ta Gombi.
Hakimin yace matasa su suke da kaso masu yawa a tsakanin al ummah don haka ya kamata a maida hankali akansu ta wajen nuna masu muhimmancin hadin kai da kuma neman ilimi wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen samar da zaman lafiya maidaurewa.
Don haka ya kamata malamai su dukufa wajen Jan hankalin matasan a koda yaushe tare da shawartan iyaye da kuma su hada tasu gudumawar wajen fadakar da matasa dangane da yadda zasu inganta rayuwarsu yadda ta kamata.
Ya kuma kirayi masu rike da masarautun gargajiya da suma sukasance masu bada hadin kai wajen wayarwa matasan kai domin ganin an samu nasaran wayarwa matasan kai yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment