An bukaci wadanda sukayi rijistan katin zabe da suje su karbaibi katin zabensu domin su samu damar kada kuri a.

An kirayi al umma musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe ta suje su karbi katinsu wanda hakan ne zai basu damar jefa kuri a a ranan zaben shekara da dubu biyu da ashirin da uku. Jami I mai hulda da jama a na hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa shiyar jahar Adamawa Dahiru Jauro ne ya yi wanan kira a lokacin da yake jawabi a wurin taron kungiyar limamai na jahar Adamawa wanda ta shirya a yola. Dahiru Jauro yace akwai mutane da dama wadanda sukayi rijista amman har yanzu basu je sun karbi katunsuba wanda kuma hakan koma bayane musammanma ga su wadanda sukayi rijistan katin zaben. Ya kuma kirayi limamai da suma su bada tasu gudumawar wajen fadakar da al umma dangane da muhimmancin katin zaben domin mallakan katin zaben shine yancinsu. Shima a jawabins malam Muhammadu Umar Zingina kiran limamain yayi da su kasance masu koyi da halayen Annabi Muhammadu (S A W) ta yadda ya gudanar da shugabancinsa ga al ummah. Malam Salihu Dauda Babban limamin Masallacin Jumma a na bayan kasuwa ya baiyana jin dadin dangane da taron da aka shirya domin wayar musu da kai dangane da yadda zasu gabatar da fadakar da al umma dangane da zaman lafiya da kuma ganin an kammala Babban zaben shekara ta 2023 cikin kwanciyar hankali ba tare da matsalaba.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie