An bukaci yan agaji su kara himma wajen taimakawa al ummah.

An kirayi yan agaji da su kasance masu da a da kuma bin umurnin shugabanni a koda yaushe domin samun cigaba dama inganta ayukan agaji harma da taimakawa al ummah. Alhaji Ibrahim Jalo ne yayi wannan kira a zantawarsa da Jarida Al Nur a lokacin da ake gudanar da horo da akeyiwa yan agaji wanda kungiyar Izala mai shelkwata a jos ta shirya a yola radar gwamnatin jahar Adamawa. Ibrahim Jalo wanda kuma kwamanda ne a wurin boron yace suna gudanar da irin wannan horone daga matakin kananan hukumomi da jahar harma da kasa baki daya. Acewarsa dai suna yin hakane domin horan da yan agajin sanin madafan aiki da kuma yadda zasu gudanar da aiyukansu cikin kwanciyar hankali ba tare da matsaloliba. Don hakqnema ya kirayi yan agaji da sukasance masu biyayya ga shuwagabani domin ganin sun samu nasara a aiyukansu. Ya kuma shawarcesu da suyi amfani da abunda aka koya musu dama fadadashi ga wadanda basu samu damar zuwa ba domin samun cigaban aiyukan agaji yadda ya kamata. Shima a jawabinsa Suleiman Tijjani Sakataren aiyukan yan agajin yace kowace shekara ne dai suke gudanarwa yan agaji irin wannan horo domin sanin yadda zasu gudanar da aiyukansu na taimakawa al umma. musammanma taimakawa marassa lafiya. Horon da ya samu halartan daukcin kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar Adamawa wanda kuma za a dauki kwanaki uku anayi wanda yake gudan a harabar makarantar kafital dake cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.