An bukaci yan Najeriya ta su zabi cancànta.

A yayinda aka cigaba da gangàmin neman zabe mukamai daban daban walau na shugaban kasa ko na yan majalisu tarayya dana jihihi harma dana gwamnoni wanda akeyi lunguna dama sako sako a fadin Najeriya. Wanda hakan yasa aka kirayi yan Najeriya da sukasance maau zaban cancanta a lokacin da sukazo kada kiri unsu. Alhaji BabaKano Jada ne ya yi wannan kira a lokaci da yake zantawa da jaridar Al Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Baba Kano yace yan Najeriya musammanmq yankin arewacin Najeriya su anifa wannan lokaci damace a garesu da su zabi wanda zai kare musu muradunsu dama cigaban yankin don haka kada suyi wa kansu sakiyar da babu ruwa wajen zaban tumun dare. Saboda haka ya kamata su baiwa Alhaji Atiku Abubakar goyon baya domin ya kashi ga samun nasara domin acewarsa shine zai kawo cigaban tattalin arziki kasancewarsa dan kasuwa kuma ya kware a siyasa. Don haka zai magance matsalar tsaro da yake ciwa al umma tuwo a kwarya. Baba Kano ya kuma kirayi matasa dake fadin Najeriya da cewa sune kashin bayan al umma don haka kar su barin wannan damar ta wucesu kasancewa Atiku ya baiyana cewa zai baiwa matasa dama a gwamnatinsa ta samar musu da aikinyi da dai sauransu. Babakano ya kara da cewa yan Najeriya sukasance masu hada Kansu da mutunta juna da kuma hakuri da juna tare kuma dayin Adu oi a koda yaushe domin neman taimakon Allah Madaukakin sarki domin ganin an kammala Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu lafiya ba tare da wasu matsaloliba. A karshe shima yayi fatan ganin an kammala gangamin neman zabe lafiya tare da kiran yan siyasa da su nisanta Kansu da aibata wasu wanda acewarsa aibata wani ba zai kaimi ga cigababa. Don haka ya kamata a kiyaye.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE