An gargadi matasa kan bangan siyasa.
A yayinda ana cikin lokacin guguwar siyasa an kirayi matasa da su nisanta kansu da bangan siyasa kuma kar su bari ayi amfani da su wajen cin zarafin wani.
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala mai shelkwata a Jos shiyar jahar Adamawa Sheik Kusa Abdullahi ne ya baiyanan haka a zantawarsa da manema labarai a yola.
Sheik Musa Abdullahi yace matasan su sanifa sune kashi bayan al umma sanan kuma sune ahuwagabanin gobe don haka kar su bari ayi amfani dasu wajen karya darajansu a idon al umma.
Suma iyaye ya shawarcesu da su kasance masu baiwa yaransu iganceccen tarbiya dama ilimi na addini da na zamani kasancewa iyaye sune suke da mujimiyar gudumawa da zasu bayar wajen tarbiyar yara.
Suma yan siyasn ya kirasu da kada suyi amfani da matsan wajen kowowa zaman lafiya barazana musammanma a wannan lokaci na gangamin yakin neman zabe da yake gudana afdin Najeriya.
Ya kirayi yan Najeriya da su cigaba da yin adu o i domin ganin an kammala Babban zaben shekar ta dubu biyu dda ashirin da uku cikin kwanciya hankali ba tare da wata matsalaba
Comments
Post a Comment