AN JA HANKALIN MANOMA WAJEN YIN ADANAN KAYAKIN ABINCI.

An kirayia manoma da su maida hankali wajen yadda zasuyi ajiya kayakin da suka noma domin kaucewa abunda zai taba lafiyar al ummah. Alhaji Adamu Jingi ne yaiyi wannan kira a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola radar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Adamu yace dazaran manomi ya kammala aikin gonarsa to yayi amfani da dabaruka da suka kamata wajen addana kayakin gonarsa. A cewarsa dai akwai Leda na musamman wanda mutum zai iya Adana kayakin nomansa ba tare da yayi amfani da sanadarin maganiba. Jingi yace yin amfani da sanadarin magani yana haifar da matsaloli musammanma a bangaren lafiya don haka ya kamata al umma sukasance masuyin taka tsantsan wajen ajiyar kayakin noma. Ya kuma kiayi manoma da su kara kaimi wajen rungumar harkokin noma domin bunkasa abinci a fadin jahar dama kasa baki daya. Harwayau Adamu Jingi ya kirayi yan Najeriya da sukasance masu hada Kansu domin yin aiki kafada da kafada domin samun cigaban kasan nan baki daya. Tare da yin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar tsaro a fadin Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE