An ja hankalin yan majalisar dokokin jahar Taraba da suyi watsi da kudirin dokan da gwamnan jahar ke kokari kai majalisar.

Daga Sani Yarima Jalingo Dan majalisar wakilai tarayara Najeriya mai wakiltan kananan hukumomin wukari da ibi a majalisar wakilain Najeriya. Hon. Danjuma Shiddi ya zargin gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku da shirin kaiwa majalisar dokokin jahar kudirin doka da zai kawowa yan jarida nakasu lamarinda ya kira da yiwa damokiradiya karan tsaye, Shiddi wanda akafi sani da Dnji s s ne ya baiyana haka a loakcinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba. A cewarsa tun daga randa yaji cewa gwamnan na yunkuri tuwa majalisar dokokin jahar kudirin dokan shine mutum na farko da ya fara Jan hankalin yan Najeriya da kada su amince da wannan doka da gwamnan ke kokarin kaiwa majalisar domin yin haka ba damokiradiyabace. Ina mai shaida muku cewa ba abida gwamna yakeso yayi illa gurgunta aikin jarida a fadin jahar Wanda kuma wannan bacigaban domokiradiya bane. Don hakanema ya kirayi takwarorinsa a majalisar dokokin jahar da suyi watsi da kudirin doka n da gwamnan ke kakarin kai musu. Dan majalisar Dan jam iyar A P C ne wanda kuma a yanzu haka dan takaran sanatane a mazaban kudanci jahar Taraba a zaben shekara ta 2023. Ya kuma koka da yadda haryazu ana cigaba ta tsare babban darektan gangamin yakin Neman zabensa wato Samaila Yakubu dama wasu mutane uku wanda kuma ya zargi gwamnatin jahar da hanu a ciki. In za a iya tunawa dai gwamna Darious Ishiyaku ya musanta duk wasu zarge zarge da ake masa dangane da tsare Samaila Yakubu. Gwamnan ya baiyana hakane ta kwamishinan watsa labarain jahar Loise Emanuel a wani taron manema labarai da ya gudanar a Jalingo fadar gwamnatin jahar Taraba. Indama yace ai an tsare Samaila Yakubu ne a Takukum bisa zarginsa da yin bangan siyasa a yankin.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE