An kaddaar da fara shirye shiryen aikin hajjin shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.

Gwamna Ahmadu Uamaru Fintiri na jahar Adamawa ya kaddakar da fara shirye shirye aikin hajjin shekara ta dubu biyu da ashirin da uku domin bada damar ganin an gudanar da aiki hajji yadda ya kamata ba tare da matsalaba. Gwamnan wanda kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Aminu Iya Abbas ya wakilta yace an kaddamar da fara shirye shirye aikin hajjinne domin baiwa hukumar yin shirye shirye akan lokaci. Ya kuma kirayi al umma musulmai da su baiwa hukumar dama gwamnatin hadin kai da goyon baya domin ganin ba a saku matsalaba a lokacin aikin hajjin na shekara ta 2023. Shima a jawabinsa Babban sakataren hukumar aikin hajji a jahar Adamawa Salihu Abubakar ya godewa gwamna Ahmdu Umaru Fintir bisa goyon baya da ya bayar wajen aikin hajjin shekara ta 2022. Wanda acewarsa an samu nasara sosai a lokacin aikin Hajjin na shekara 2022. Da yake nashi jawabi shugaban hukumar aikin Hajjin a jahar Adamawa Ustas Bappari Umar Kem shima godiyayiwa gwamna bada hadin kai da goyon baya da yakeyi a lokacin da ake gudanar da aikin hajji kuma ya nuna jin dadinsa dangane da yadda aka kaddamar da fara aikin hajjin akan lokacin wanda acewarsa hakan zai baiwa hukumar damar shirye shiryen da ya kamata domin gudanar da aikin hajjin shekara ta 2023. A jawabinsa Sarkin Shelleng Amna Shelleng Abdullahi Isa Dasong kiran al umma musulmai yayi da su kasance masu baiwa hukumar hadin kai da goyon baya domin ganin hukumar ta cimma nasara a duk lokacin da ake gudanar da aikin hajji.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE