An kirayi al umma fulani musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe da suje su karbi katin zabensu.

An kirayi al umma Fulani muasqmmanma wadanda sukayi rijistan katin zabe da suje su karbi katin zabensi domin hakan ne zai basu damar wamda zai cire musu kitse a wuta. Alhaji Sa idu Maikano kuma shugaban matasan Fulani a Najeriya ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Alhaji Sa idu Maikano yace al umma Fulani suna da kuri a masu yawa saboda haka ya kamata suje su karbi katin su wanda a yanzu haka hukimar zabe mai zaman kanta ta kasa ta cigaba da bayarwa a dukkanin cibiyoyinta dake fadin kasan nan. Alhaji Sa idu yace ya kamata al umma Fulani su sani kuri arsu tana da muhimmanci domin da shine zasu zabi shugaban da sukeso wanda suke ganin zai iya magance masu matsalolinsu. In kuma basu da kuri a to zasu zama yan kallo. Saboda haka ya kamata su gaggauta zuwa cibiyoyin hukumar zaben domin karban katin su wanda hakan zai kare musu mutuncinsu da kuma yancinsu yadda ya kamata. Ya kuma shawarci al umma Fulani musammanma matasa da su nisanta kansu daga bangan siyasa dama duk abunda zai kawo tashin hankali a tsakanin al umma domin samar da zaman lafiya dama cigaban kasan nan baki daya. Harwayau ya kirayi yan Najeriya da su cigaba dayin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshe dukkanin kalunalen tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.