An kirayi Babban bankin Najeriya da yayi la akari da kanaan yan kasuwa kan kayyade kudi da za a iya cirewa a yini.

A cigaba da koke koke da akeyi dangane da yadda Babban bankin Najeriya kayyade yadda dai dai kum mutane dama kakfanoni zasu rinka cirewa a yin ko mako wanda ya kama daga dubu dari zuwa dari biyar wanda hakan yasa kungiyar yan kasuwa a rewacin Najeriya ta nuna damuwarta dangane da lamarin. Shugaban kungiyar yan kasuwa a arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne ya baiyana haka a wata tattaunawa da yayi da jaridar Al Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Muhammed Ibrahim 86 yace Babban bankin na Najeriya baiyi la akari da yan kasuwa dake karkaraba wadanda yawancinsu basu da asusun ajiya a bankuna don haka wannan mataki na Babban bankin Najeriya zai iya nakasa harkokin kasiwancin karkara. Saboda haka ya kamata Babban bankin yasake nazari domin kara yawan kudi da za a cire a yin ko a mako. Alhaji Ibrahim yace ga misali mutum yaje ya sayi saniya a kasuwar karkara to ta yaya zai biya kudin tunda mai saniya bashi da asusun ajiya a banki kai kuma ba abaka damar cire kudi mai yawaba to yaya saka sami kudin biya. Don haka akwai bukatan a sake duba lamarin domin yin gyara. A cewar Ibrahim 86 yawancin yan kasuwan arewacin Najeriya kanan yan kasuwa ne saboda ya ya kara jaddada kirasan sa da Babban bankin Najeriya da ya faddad yadda za a rinka cire kudin daga dai dai kum mutane har ga zuwa kamfanoni domin bunkasa harkokin kasuwancin a yankin na arwacin Najeriya. Ya kuma kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shiga tsakani domin magance koke koke da akeyi dangane da aniyar Babban na Najeriya domin sauwakawa yan kasuwa musamma kananan yan kasuwa. Ya kara da kiran yan Najeriya da su cigaba da yin adu oi domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo krshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya. Tare da ganin an kammala Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku lafiya ba tare da matsalolinba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE