An kirayi gwamnatin jahar Taraba da ta baiwa bangaren wasanni muhimmacin.

Daga Sani Yarima Jalingo. A yayinda aka kamala gasar kwallon kafa na Delta National Sport Festival an kirayi gwamnatin jahar Taraba da ta baiwa sashin wasanni muhimmaci domin samun cigaban harkokin wasanni a fadin jahar. Wasu yan wasan kwllon kafa wato Mr Joseph Yohana, Jerry Jermiah da magiyin bayan wasanni Isa Bilal a zantawarsu da manema labarai a Jalingo dangane da kammala wasanin Delta National sports Festival wanda aka gudanar a Asaba fadar gwamnatin jahar. Mutanen dai sun baiyana rashin jin dadinsu dangane da yadda gwamnatin jahar ta Taraba ta nuna halin ko inkula da bangaren wasanni da matasa a fadin jahar. A inda sukce gwamnatin tsohon gwamnan jahar ta Taraba wato Rev. Jolly Nyame ta taka rawan gani wajen inganta sashin wasanni a jahar, wanda hakan yasama filin wasanni jahar yana daya daga cikin wadanda skayi fice a fadin Najeriya. Saboda haka nema suke zargin gwamnati maici a yanzu da rashin katabus a bangaren wasanni tun daga tsofuwar gwamnatin mari gayi Danbaba Suntai. Da yake maida martani dangane da zargin rashinyin abun azo a gani da gwamtin keyi a bangaren wasanni kwamishin wasanni da matasa a jahar Taraba Hon. Hassan Bappa wannan zargi ba gaskiyaace saboda gwamnati tana iya kokiarinta na ganin an buniasa harkokin wasanni a fadin jahar Taraba baki daya. Hassan yace ai ko wasanni da aka kammala a jahar Delta gwamnatin ta bada kudade domin ganin an samu nasara. Don haka gwamnati ta daura damaran ganin an inganta harkokin wasanni a fadin jahar baki daya. A ranan Jumma an ne aka kammala wasanni da akayi a Asaba inda jahar ta samu tagulla uku kamar yadda darektan wasannin jahar Taraba George shitta ya baiyana a zantawarsa da anema labarai a filin wasa Stephen Keshi dake Asaba inda anan nema aka gudanar da wasannin.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.