An kirayi iyaye da sukasance masu sauke hakkin yaransu.

Dangane da bada inganceccen tarbiya ga yara an kirayi iyaye da cewa sune suke da kaso mafi yawa wajen baiwa yaransu tarbiya. Don haka dolene su tashi tsaye domin sauke hakkin da Allah ya dora musu kan kula da yaran. Shugaban kungiyar Attarahum Foundation a jahar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ne ya yi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Mallam Muktar Dayyib yace iyaye susanifa Allah madaukakin sarki zaitambayesu yadda suka tarbiyatar da yaran su domin Amanan yaran ne Allah ya basu. Don haka ashe bai kamata ace iyaye sunyi wasa da tarbiyar yaransunba. Saboda haka su sani yaran suna da hakki akansu kuma dole ne Allah madaukakin sarki za tambayesu hakkin da aka basu. Saboda haka baiga dalilinda yasa iyaye zasu rika yin sakaci da tarbiyar yaransuba. Ya kuma kirayi malamai da sukasance masu wayarwa al umma kai dangane da irin muhimancin tarbiyar yara da kuma illar rashin tarbiyar yaran wanda acewarsa haka zai taimaka wajen samar da inganceccen tarbiyar yaran a tsakanin al umma. Mallam Muktar ya kuma shawarci iyaye da su hada kai da al umma wajen tarbiyar yaran da kuma sanin irin yaran da yaran su ke mu amala da su domin ganin yaran basu gurbaceba. Akarshe ya kirayi iyaye da su maida hankali wajen yiwa yaran nasu adu oi a koda yaushe tare da musu fatan Alheri wanda haka yana muhimanci kasancewa adu o i iyaye yana tasiri sosai dangane da yaran.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.