An samu hatsarin mota a tsakanin Mayo Belwa da Jada.
An samu hatsarin motoci biyu akan hanyar dake tsakanin karamar hukumar Mayo Belwa da karamar hukumar Jada dake jahar Adamawa a daren litinin da tagabata.
Shadar gani da ido Muhammad Sani Jada ya tabbatarwa Jarida Al Nur cewa lamarin ya farune a tsakanin wata motar daukan kaya da kuma karamar mota.
Kawo yanzu dai ba asan abunda ya haddasa hatsarinba sai dai anfin daganta yawan hatsari na faruwa sakomakon yawan gudu ko kuma rashin kyaun hanya.
A yanzu haka dai mutum dayane aka tabbatar ya samu rauni sakamokon tsarin.
Comments
Post a Comment