An shawarci manoma da su maida hankali wajen amfani da inganceccen iri.

An shawarci manoman Auduga da su bukasa noman auduga ta amfanin da inganceccen iri domin samun wadaceccen auduga wanda hakan zai taimaka wajen samar da kudin dama aikinyi a tsakanin matasa. Ko odinatan hukumar inganta fasahar iri a Najeriya Dr Rose Maxwell Gidado ce ta baiyana haka a zantawarta da Jaridar Al Nur a yola. Dr Rose tace noma auduga yana da muhimmanci musamamma wadanda aka inganta iri domin yana dauke da sanadarin kariya daga kwari kuma baya bukatàr feshi da yawa sannan yana jibre fari ga kuma samar da ishesheshen auduga. Ta kuma ce a yanzu noma auduga ya taimakawa ta wajenn yin abubuwa masu yawa da suka hada da biyan bukatun manoma auduga da kuma yin amfani da audugan wajen yin sake sake da dai sauransu. Don haka tace manoma bai kamata suyi da wasaba wajen rungumar harkokin noma auduga wanda acewarta hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki kasa baki daya. A bangaren sauran irin da suka hada na shinkafa, masara, sukam ana daf da kammala aiyuka akansu domin yamzu ana matakin gwajine kuma na bada dadewaba za afara bayarwa manoma dake fadin kasannan baki daya. Abangaren iri wake kam an kammalashi wanda a yanzu hakama manoma da dama suna shukawa a gonakainsu kuma suna samun amfani sosai. Saboda haka neka take kira ga gwamnati a dukkanin matakai da sukasance masu taimakawa manoma musammanma na yankunan karkara domin ganin an bunkasa hakokin noma yadda ya kamata afadin Najeriya baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE