An shawarci masu gina makarantun Islamiyoyi da su rinka maida hankalin kan makarantun.
An shawarci masu gina Islamiyoyi da su mada hankali wajen inganta gina islamiyoyi da ma diban malamai masu karantarwa domin inganta karantarwa makarantn Islamiyoyi yadda ya kamata.
Shugaba kungiyar Majalisar Islamiyoyi a jahar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da Jaridar Al Nur a yola.
Mallam Muktar yace ana fuskantar matsaloli da dama a cikin makarantu Islamiyoyi don haka dole a maida hankali wajen daukan malamai da zasu karantar a makarantun.
Acewarsa dai makarantu Islamiyoyi sune ginshikin karantar da yara saboda haka ya zama wajibi a inganta makarantu ta karantarwa da kuma suwaye ne zasu karantar a makarantu.
Mallam Dayyib ya kirayi malamai musammanma masu karantar da Islamiyoyi da su sanifa an basu amanan karantar da yarane don haka baikamata suci amanaba.
Ya kuma kirayi iyayen yara da suma sukasance suna bada tasu gudumawar ta buyar kudin makarnta yaransu akan lokaci da kuma hada kai da malamai wajen baiwa yaran tarbiya yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment