An shawarci mata musammanma wadanda sukayii rijistan katin zabe da suje su karbi katin zabensu.

An kirayi mata musammanma wadanda sukai rijistak katin zabe da suje cibiyar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa domin karban katin zabensu wanda haka zai basu damar shuwagani da suke so a ranan zabe. Shugaban kungiyar mata musulmai ta tarayya FOMWAN shiyar jahar Adamawa Hajiya Khadija Buba ce ta yi wannan kira a zantawarta da jaridar All Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Hajiya Khadija Buba tace yana da muhimmanci duk wanda tayi rijstan katin zabe to kada ta yi da wasa wajen kabar katin domin ganin itama ta shiga sahun masu zabe a shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Hajiya Khadija ta shwarci mata da subi dukkanin dokokin da suka dace a wajen karban katin tare da gaggauta karba saboda hukumar zaben ta fara bada katin zaben ne daga watan disemba wanda kuma zata rufe karba katin a ranan ashirin da biyu ga watan janairu shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Ta kirayi matan da kada wasu su rudesu su karbe katun zabensu kada kuma su sayar da katin nasu domin sayar da katin kamar sayar da yancine saboda haka mata suyi hattara. Hajiya ta kuma shawarci mata iyaye da sukasance masu lura da yaransu musammanma a wannan lokaci na guguwar siyasa da su maida hankali ta wajen mu a malarsu da jama a da kuma sanin in zasuje kuma da su wa suke mu amula. Wanda acewarta haka zai taimaka wajen kare yaran daga shiga halinda bai daceba. Ta kuma kirayi malamai da su dukufa wajen fadakar da al umma muhimkancin yin zabe dama karban katin zaben domin a cewarta katin zaben yana matukan muhimmanci. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tasha kokawa dangane da yadda jama a musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe basa zuwa karban katin na su duk da cewa anata kiraye kiraye cewa duk wanda ya yi rijista da yaje ya karbi katinsa. Kawo yanzu dai hukumar zabe tace akwaikatin zaben masu yawa wadanda ba a karbesuba. Harwayau ta kirayi yan Najeriya da su baiwa hukumar zaben hadin kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran gudanar da zabe mai inganci a babban zaben shekara ta 2023. Tare kuma da yin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin matsalar tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.