An shawarci matasa su daina furta kalamain batanci a shafukan sada zumunta.

An shawarci matasa musammana wadanda ke amfani da dandalin sada zumunta da su kasance masu wallafa abunda zai amfani Al umma su kuma kaucewa duk wasu kalamain batanci a shafukan sada zununta. Alhaji Salihu Baba Ahmed ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da jaridar Al nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Salihu Baba Ahmed yace ba daidaibane a rinka furta kalamain batanci akan wasu wai da sunan yancin fadin albarkacin baki domin shi wanda akayiwa batanci shima yana da yanci, saboda haka al ummah su nisanta kansu da cin zarafin wasu. Ya kuma kirayi iyaye da suma su bada tasu gudumawar wajen Jan hankalin yaransu domin ganin ba a samu irin wadanan matsalaba. Tare da kiran shuwagabanin musammanma wadanda lamarin ya shafa sukasance masu hakuri da yafiya domin samun cigaban zaman lafiya. Don haka nema Salihu Baba Ahmed ya yabawa uwar gidan shugabĂ n kasa Aisha Buhari bisa yafiya da tayiwa matashinan Aminu Muhammed biyo baya cin zarafin ta da yayi a shafuka sada zumunta wanda acewarsa ta nuna ita uwace wanda take da tausayi.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE