An shawarci ya yan jam iyar APC a jahar Adamawa da su hada kansu domin ganin sun samu nasara a zabe mai zuwa.

An kirayi yan Jam iyar APC a jahar Adamawa da sukasance masu hada Kansu domin siyasa bata "ayi ko a mutu bane" ana siyasa ne domin samun ci gaba da kuma bunkasa dukkanin abunda zai kawo ci gaban al-umma, dama kasa baki daya. Alhaji Sani Jada ne yayi wannan kira a zantawarsa da Jaridar Al Nur a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Muhammadu Sani Jada yace a daina nuna banbacin kabilanci ko addini a siyasa, wanda acewarsa yin haka ba zai haifarwa kasan Da mai idoba, sai dai ya kawo koma baya a harkokin siyasa da bata zamantakewan Jama'a da dai sauransu. Ya kara dacewa banbance banbace da rashin hadin kai ne yasa Jam iyar APC bata samu nasaraba a zaben shekara da dubu biyu da sha tara da ya gabata. Don haka dolene Jam iyar ta APC ta kasance ta dinke duk dukkanin matsaloli da take ciki domin ganin ta samu nasarar lashe kujeran gwamna a zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Alhaji Sani Jada yace saboda irin aiyukan cigaba da suka gudanar a jahar musammanma a lokacin gomnatin APC karkashin Vice Admiral Mutrala Hamman Yero Nyako cikin shekaru bakwai Musamman a fanning horar da matasa sana'oi daban daban wanda hakan yasa har yanzu suna da magoya baya sosai don hakane yake gani ba wani haufi Jam'iyar A P C zata yi nasara a babban zabe mai zuwa da yardan Allah. Alhaji Sani Jada ya Kara da cewa, a lokacin gomnatin APC karkashin shugabancin Baba Mai Mango, Wato Nyako, an Samar da Kananan Asibitoci watau Primary Health Care a tsakani gundumin Siyasa guda 226 na Jihar Adamawa, an Samar da Magunguna kauta ga Jarirai har zuwa shekaru biyar da haifuwa, Mata na haifuwa kauta adukkan Asibitocin Jihar Adamawa, an Samar da hanyoyi a kalla kilomita biyu a ko wace Karamar hukar Jihar Adamawa, An Samar da Babban Asibiti na German Hospital a Yola, an Samar da tallafin da su ke kira SA ma dubban Matasa da Mata, an sare da Gonakin gwaji domin koyawa Manoman noma irin na zamani, an gida sabbin ajujuwa kimanin Dubu biyar ciki har da gidajen Samar a Makarantu, an yi koskwariman ajujuwa fiye da Dubu biyar a Jihar Adamawa. Ga Samar da ruwan Sha da Jama'a da Dabbobi. Alhaji Sani Jada ya Kara cewa, da duk wannan dubbin alheri, ta yaya gomnatin RIKO na PDP zata kayar da APC a Adamawa. Ya kuma Jadada da shawa kan Magoya bayan APC su kasance masu hada kansu kuma da su Kai zuciya nesa da hakuri da wanda duk Allah ya basu mulki, domin Allah ne ya ke bada mulki ga wanda yaso a lokacin da Ya so Kuma Ya karbe a lokacin da Yakeso, don haka bai kamata ace ana tada jijiyar wuyaba ga wanda Allah ya baiwa mulki. Alhaji Sani yace Jam iyar A P C taga illar rashin hadin kai a zaben shekara ta dubu biyu da sha tara wanda haka ne ya kaita ga rasa kujeran gwamna don haka ya jaddata bukatar a hada kai domin ganin jam iyar ta samu nasara a dukkanin kujerun siyasar jahar baki daya. Alhaji Sani Jada ya kuma yi fatan ganin an kammala zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku lafiya ba tare da hatsaniyaba. Tare da baiwa Matasa shawartar da kada su bari ayi amfani da su wajen tada hankali a lokaci dama bayan zabe. Da wannan nema yake shawartan daukacin yan Najeriya da su dukufa wajen yin adu'o'i domin neman taimakon Allah Madaukakin Sarki wajen kawo karashen dukkanin kalu balen tsaro a fadin kasan nan baki daya. Idan zaku tuna Alhaji Muhammadu Sani Jada ne ya jagoran ci fanin horar da Matasa Maza da Mata a sana'oin Hannu dababan suka Kuma yaye daliban da kayan guda nar da sana'ar da suka koya keuta a locin gomnatin Baba Nyako, Baba Mai Magoro cikin shekaru bakwai, watau daga 2007 har zuwa 2014.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE