Gwamnatin jahar Adamawa tace tana cigaba da wayarwa al ummah kai dangane da illar cin zarafin biladama.
Gwamnatin jahar Adamawa na cigaba da kokarin wayar da kan al’ummar dangane illar cin zarafin jinsi wato GBV.
Kwamishiniyar ma’aiakatar harkokin mata da ci gaban more rayuwa, Misis Lami Patrick ce ta baiyana haka yayin wani zaman tattaunawa kan batun da ya mamaye duniya mai taken KAWO KARSHEN CIN ZARAFIN MATA DA YARA MATA KANANA, domin kaddamar da ranaku 16 na gagwarmaya a Jahar Adamawa, hukumar ci gaban raya kasa da kasa ta kasar Amurka. USAID ce ta shirya a birnin Yola, fadar jahar.
Komishiniyar ma’aikatar harkokin mata da ci gaban more rayuwa, Misis Lami Patrick wanda ta samu wakilci jami’in ofishin bada kariya na ma’aiakatar, Hassan Aliyu yayin tattaunawar tace, a kokarin gwamnatin jahar na kawo karshen cin zarafin jinsi a jahar, ta samar da wani cibiyar kai koke, wato one stop referral centre, kari kan wadanda take da su a fadin jahar.
Komishiniyar tace, ma’aikatar ta ziyarci kananan hukumomi tara daga cikin ashirin da daya da ake da su domin wayar wa al’umma kai kan cin zarafin jinsi dama sabon dokar nan na kare wanda aka cin ma zarafi, wato VAPP ACT wanda gwamna ya rattaba wa hannun kwanannan.
Ta kuma godewa USAID STATE2STAE da shirya wannan zama wanda a cewar ta zai taimaka wajen tattauna kan yadda za a bullo da hanyoyi da za su kai ga kawo karshen cin zarafin jinsi a fadin jahar.
Itama shugaban kungiyar GOGGOJI ZUMUNCI INITIATIVE, kungiya mai zaman kanta, Hajiya Aishatu Yakubu tace zaman tattaunawan ya zo a daidai lokacin da ake bukata domin hakan zai baiwa bangaren gwamnati da kungiyoyin fararen hula da duk masu ruwa da tsaki damar zaman domin tattauna yadda za a kawo karshen cin zarafi a cikin al’umma, tare da godewa USAID STATE2STATE da samun lokaci domin hade dukkan masu ruwa da tsakin wajen wannan tattaunawa.
Shima shugaban hadaddiyar kungiyoyin masu bukata ta musamman ta kasa reshen jahar Adamawa, Injiniya Sani Sabo y ace taron taattaunawan bai yi latti ba domin yawancin masu samun kansu a yanayin cin zarafi masu bukata ta musamman ne wadanda basu da wani dabara na kare kawunan su.
Injiniya Sabo ya kuma kirayi gwanmantin da mai girma gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ke jagoran ta data gaggauta samar da hukuma kula da masu bukata ta musamman kamar yadda ta dau alkawari yayi darewar ta karagar mulki.
Taron zaman tattaunawar dai ya samu hallattan jami’an gwamnati da kungiyoyin faraen hula, da ma muhimman masu ruwa da tsaki domin tattauna batutuwa da suka shafi cin zarafin jinsi, da ma hanyoyi da za a iya bi domin kawo karshen cin zarafi a cikin al’umma.
Comments
Post a Comment