Kakakin majalisar dokokin jahar taraba yayi murabus.
Daga Sani Yarima a Jalingo.
Rahotanni daga jahar Taraba na baiyana cewa kakakin majalisar dokokin jahar wato Rt Hon Farfesa Joseph Albasu Kunini yayi murabus daga mukaminsa.
Kakakin majalisar ya yi murabus dinne a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin jahar a laraban nan. Wasikan wanda mataimakin kakakin majalisar Hamman Adama ya karanta a zauren majalisar wanda kuma shine ya jagoranci zaman majalisar. Inda yace kakakin majalisar yayi murabus din ne bisa radin kansa.
Kawo yanzu dai shugaban kwamitin ilimi a majalisar kuma shugaba mai tsawatarwa John Kizito Bonzena wanda yake wakiltan Zing a majalisar shine aka zaba a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin jahar ta Taraba.
Da yake yiwa maema labarai jawabin Jin kadan da kammala zaman majalisar sabon kakakin majalisar Hon John Kizito Bonzena ya murabus din da kakakin yayi ba zai shafi harkokin siyasar jaharba. Yace duk da cewa Kunini ya yi murabus din ne bisa radin kansa, amman har yanzu shi membane a majalisar dokokin jahar.
Ya kara da cewa zasuyi dukkanin abunda ya kamata domin ganin sun gudanar da aiyukan cigaban jahar a tsakanin watanni da suka rage.
Comments
Post a Comment