Kungayar Arewa Decide ta sha alwashin gain Atiku Abubakar yayi nasra a zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Kungiyar Arewa Decide ta sha alwashin ganin dan takaran shugaban kasa a karkashin Jam iyar P D P Alhaji Atiku Abubakar ya lashen zaben shugaban kasa a babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Kungiya ta baiyana hakane a wani gangamin nuna goyon bayanta ga Atiku wanda aka gudanar a cikin garin Jimeta a karamar hukumar yola ta arewa radar gwamnatin jahar Adamawa.
Da yake yiwa manema labarai jawabi ko odinaton kungiyar a jahar Adamawa Ahmed Bello yace sun shiraya wannan gangamin ne domin nuns goyon bayansu ga Alhaji Atiku Abubakar ganin shi dan yankin arewacin Najeriya ne. Don haka suka ga ya kamata su maramasa baya, domin ganin ya samu nasara.
Ahmed ya kara da cewa sukam a shirye suke subi dukkanin hanyiyin da suka dace na ganin cewa Alhaji Atiku Abubakar ya kai ga samun nasara cikin kwanciyar hankali ba tare da matsaloliba. Wanda acewarsu Atiku ne zai ceto su ta sama musu aikinyi da kuma magance matsalar tsaro a fadin kasan nan baki daya.
Don haka nema Ahmeda Bello ya kirayi yan Najeriya musamman ma matasa da su sanifa wanna damace a garesu na marawa Atiku baya ganin yadda ya sha alwashin baiwa matasa fifiko in har yayi nasaran zama shugaban kasa. Saboda haka karsubari wannàn damar ta kubuce musu.
Ya kuma shawarci matasa da su nisanta kansu dayin bangan siyasa domin kaucewa tashin hankali a lokaci dama bayan zabe domin cigaban Najeriya baki daya.
Gangamin dai ya hada kan al umma da dama da suka fito daga cika da wajen fadar gwamnati da suka hada maza da mata inda suka fara daga makarantar Kafital zuwa sha tàletalen mai dogi har zuwa sha taletalen Mubi da ke cikn garin Jimeta.
Kawo yanzu dai yan siyasa da ke neman mukamai daban daban ne dai suka bazama lunguna da sako sako dake fadin Najeriya domin neman kuri un Jama a a ranan zaben shekara ta 2023.
Comments
Post a Comment