Kungiyar hadakan mabukata na musamman ta koka dagane da yadda ba adamawa dasu a gwamnatin jahar Adamawa.

Kingiyar hadaka na abukata na musamman a jahar Adamawa sun koka da yadda gwamnatin ke nuna musu wariya a harkokin gwamnati duk da cewa suma suna da irin nasu gumawar da zasu iya bayarwa na cigaban jahar. Shugabna hadakar kunhiya a jahar Adamawa Injiniya Sani Sabo ne ya baiyan haka a wajen wani taro wanda hukukmar raya kasa da kasa na kasar Amurka wato USAID ta shirya a wani mataki na ranan manukata na musamman ta duniya mai taken inganta tare da dina nunawa mabukata na musamman wariya anan yola. Sani Sabo yace gwamnatin jahar tayi burus da su wajen daukansu aiki harma da kula da walwalansu wanda acewarsa suma suna da gudumawa da zasu iya nayarwa wajen cigaban jahar harma da tattalin arziki. a jahar dama kasa baki daya. Ya kuma godewa hukumar ta USAID bisa shirya wannan taron domin tabbatar da cewa mabukata na musamman za a iya damawa dasu a harkokin duniya baki daya. Shugabar tawagan jahar Adamawa a wajen taron Hajiya Maryam Dikko race manufar taron dai itace ganawa da mabukata na musamman domin sanin yadda za a aiwatar da dokan da ta shafesu a fadin jahar. Hajiya Maryam ta kiyesu da suyi amfani da abunda sukaji a wurin taron domin samun cigaban kungiyar tasu baki daya. A nata jawabi kwakishiniyar Ma aikatar harkokin mata a jahar Adamawa misis Lami Patrick wanda Jami in kariyana ma aikatar Hassan Aliyu ya wakilta ta kirayi mahalarta taron da sukasance masu hada Kansu da kuma marawa gwmnati baya wajen gudanar da tsare tsren cigaban jahar. Ta kuma yabawa hukumar ta USAID dangane da shirya irin wannan taro tare dashwartan mahalarta taron da suyi amfani da abunda aka koya musu domin samun cigaban kungiya dama yayan kungiyar a kasa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE