Kungiyar Izala ta aurar da marayu ashirin a jahar Adamaww.
An kirayi mawadata da su rinka taimakawa marayu a koda yaushe domin samun fafalan Allah madaukakin sarki da kuma samun dukiya mai albarka dama samun rabao ranana gobe kiyama.
Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheik Abdullahi Bala Lau ne ya yi wannan kira a lokacinda ya jagoranci daurin auren marayu ashirin wanda akayi a Babban Masallacin Jumm a dake Daubeli a cikin karamar hukumar yola ta arewa dàke jahar Adamawa.
Sheik Abdullahi Bala Lau yace taimakawa maryu yana da mutakan muhimmani da kuma samun dinbin lada daga wurin Allah don haka ya kamata masu hanu da shuni sukasance masu maida hankali wajen taimakawa marayu domin suma su samu walwala a tsakanin al umma.
Ya kuma kirayi al umma musulmai sukasance masu hada Kansu da kuma gudanar da adu o i wanzar da zaman lafiya tare da tausayawa juna wanda hakan zai taimaka wajen cigaban addinin musulunci baki daya.
Ya kuma shawarci marayu musammanma wadanda aka daura musu auren da sukasance masu tsoron Allah da kuma hakuri da biyayya wanda avewarsa haka zai basu damar moriya anan duniya dama gone kiyama.
Shima a jawabinsa shugaban kwamitin marayun Alhaji Usman Ibrahim ya yabawq membobin kwamitin bisa kokari da sukayi har yakai ga auran da marayun don haka nema ya shawarcesu da sucigaba da irin wannan na mijin kokari da sukeyi domin taimakawa marayun a koda yaushe.
Ya kuma shawarci al umma da su kara himma wajen taimakawa domin kula da rayuwar marayun yadda yakamata.
Andai gudanar da daura auren marayu ashirin din ne bisa sadaki nera da dubu hamsin kowannensu da kuma kayakin daki da dai sauransu.
Comments
Post a Comment