Kungiyar mafarauta NHFSS ta lashi takwabin inganta tsaro a dajuka.

Daga Ibrahim Abubakar yola. A wani mataki na magance matsalar tsaro kungiyar mafarauta da inganta tsaron daji a Najeriya wato NHFSS a takaice shiyar jahar Adamawa ta sha alwashin kauda dukkanin ta addanci a cikin daji baki daya. Kwamandar kunguyar mafarauta wato NHFSS Aisha Bakari Gombi ce ta bayana haka a taron da kungiyar ta gabatar a yola. Kwamandan tace a shirye suke su shiga dajin dake fadin kasan nan domin fatattakan masu aikata lafuka a daji da kuma dakile aiyukansu baki daya. Tace yanzu lokaci yayi da baza a nade hanu a barwa gwamnati komaiba don haka ya kamata al ummah su bada hadin kai da goyon baya domin ganin an cimma nasaran kawo karshen matsalar tsaro baki daya. Ta kuma baiyana cewa kungiyar a ahirye take ta hada kai da dukkanin hukumomin tsaro domin tabbatar da ganin an kare rayuka dama dukiyoyin al ummah. Mai martaba Lamido Adamawa Dr Muhammed Barkindo Aliyu ya yabawa kungiyar mafarautar bisa wannan na mijin kokari da sukeyi na kawar da aiyukan batagari a cikin daji wanda kuma hakan zaitaimakawa al ummah kasa bakai daya. Shima a jawabinsa AC Admin A jahar Adamawa Hassan Adamu yace sunma horas da Jami ansu kama daga matakin jahar har zuwa anguwanni. Anashi bangaren maibaiwa kwamandan shawara a bangaren shariya Barista Aliyu Bawuro ya kirayi majalisar dokokin ta kasa da su gabatar da kudirin doka da zai baiwa mafarauta damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata. Kungiyar ta kuma kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samar da dokan da zai inganta aiyukan mafarautar a fadin Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE