Kungiyar masu P O S a jahar Adamawa sun koka kan matakin Babban bànkin Najeriya na kayyade kudin da za a cire a rana,
Kungiya ma aikatan P O S a jahar Adamawa sun koka dangane da aniyar Babban bankin Najeriya kan kayyade kudin da daidaikun jama a ko kamfani zasu iya cire a yin zuwa mako, dai daikun mutane suna iya cire dubu ashirn a yini sai kuma kamfani zai iya cire dubu dari biyar kacal a mako lamarinda ya haifar da maida martani daban daban.
Shugaban masu P O S a jahar Adamawa Alhaji Auwal Usman shugaban kamfanin Auwalus Business Concept ne yabaiyana koken nasu a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Alhaji Auwal yace basuji dadin wannan lamariba ko kadan don haka nema yake kira ga Babban bankin Najeriya da ya sauya wannan tunani nashi ya duba irin yana yi da ake ciki na wahalar rayuwa. Domin wanan tsari zai sake jafa mutane cikin mawuyacin hali musamman ma su masu aikin P O S wànda kuma zai shafesu ta fannoni daban daban.
Auwal kuma kirayi wakilain al umma musammanma yan majlisu da su taimaka su takawa Babban bankin na Najeriya birki dangane da aniyarsa na sanya dokan kayyade cire kudi.
Ya kuma kirayi gwamnatin tarayya da ta duba wannan lamari ta daukin matakin sausautawa al umma domin su samu saukin rayuwa domin wannan doka da Babban bankin Najeriya ya dauka bai daceba.
Harwayau Auwal Usman ya kirayi yan Najeriya da su kasance masu hada kansu da kuma yin adu oi samar da zaman lafiya mai daurewa a fadin Najeriya baki daya.
Comments
Post a Comment