Kungiyar Tabbutal Pulaku Jamde Jam ta sha alwaahin kawo karshen rikiici a tsakanin manoma damakiyaya a jahat Adamawa.

Kunhuyar Tabbutal Pulaku Jamda Jam Foundation dake jahar Adamawa ta kudiri aniyar kawo karshen rikici a tsakanin manoma da makiyaya fadin jahar Adamawa baki daya. Mataimakin shugaban kungiyar Tabbutal Pulaku Jamde Jam Foundation a jahar Adamawa kuma Ardo Fulanin Gwalamba Hassan Ali Soja ne ya bayana haka a likacin da take zantawa da jaridar Al Nur a yola. Hassan Ali Soja yace ko shakka babu zasuyi dukkanin abinda ya dace domin ganin an magance duo wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya domin samun damar bunksa harkokin noma a fadi jahar dama kasa baki daya. Don haka nema ya kirayi manoma da makiyaya da su sanifa su yan uwan junane saboda haka sukasance masu hada Kansu a koda yaishe domin ganin rikici a tsakanin manoma da makiyaya ya zama tarihi. Hassan ya kuma kara da cewa yanzu haka suna iya kokarin ganin sun samar da burtiloli domin baiwa dabbobin hanya kamar yadda gwamnatin tarayya ta bukaci haka. Da wanna nema yake shawartan manoma da makiyaya da su basu hadin kai da goyon baya domin ganin sun cimma nasaran dikile rikici a tsakanin manoma da makiyaya baki daya. Ali Soja yace jahar Adamawa ta taka rawan ganin ganin cewa a shekaru biyu da suka gabata ba a samu rikici a tsakanin manoma da makiyayaba don haka da yardan Allah madaukakin sarki kungiyar tasu zatayi dukkanin mai yiwa wajen kawo karshen matsàlar baki daya. Ya kuma kirayi sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro da suma su bada tasu gudumawa wajen dauka matakin kawo karshen ta kaddama a tsakanin manoma da makiyaya wanda a cewarsa hakan zai kawo cigaba sisai a bangaren noma dama kiwo. A katshe ya shawarci manoma da makiyaya da su cigaba da yin adu o i a koda yaushe domin neman yaimakon Allah ma daukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin jahar dama kasa baki daya. Rikici a tsakanin manoma da makiyaya dai yakanyi sanadauyar Asaran rayuka dama dukiyoyi masu yawa dama muhalin duk da kokarin da gwamnati keyi na magance matsalar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE