Kungiyar yan kasuwar arwacin Najeriya ta yabawa Babban bankin Najeriya .

Kungiyar yan kasuwa na yankin arewacin Najeriya ta yabawa Babban bankin Najeriya bisa sauya dokan kayyade cire kudi gaga Naira dubu dari a mako ga daidaikum jama a zuwa dubu dari biyar a mako a yayinda kamfanoni kuwa daga dubu dari biyar a mako zuwa milyon biyar. Shugaban kungiyar yan ksauwa na yankin arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar Al Nur a yola.
Alhaji Ibrahim 86 yace Babban bankin na Najeriya yayi dai dai da ya saurari koke koken jama a dangane da lamarin kuma ya janye dokan cire kudin da yasa tunda farko don haka wannan cigabane sosai. Wanda kuma hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa yadda ya kamata. Alhaji Ibrahim yace hakan zai taimakawa kananan yan kasuwa da matsakaitar yan kasuwa samun damar bunkasa kasuwancinsu ba tare da wasu matsaloliba. Don haka nema ya kirayi yan kasuwan da sukasance masu baiwa tsare tsaren gwamnati hadin kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na bunkasa harkokin kasuwanci a fadin Najeriya baki daya. Ya kuma kara da cewa yan kasuwan su sanifa batun kaiyade cire kudi da Babban bankin yayi zai taimaka wajen rage cutar jama a da kuma taimakawa domin cigaban hada hada kudade dama kare darajan kudin Najeriya. Musammanma a wannan lokaci da komai ya koma na zamani. Harwayau ya kirayi gwamanatin tarayya da ta kasance maijin koke koken al umma da kuma tallafasu ta fannoni daban daban wanda acewarsa haka zai kawo cigaban bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya. In za a iya tunawa dai Babban bankin Najeriya ya sanya dokan kayyade cire kudi kama daga daidaikim jama a zuwa kamfanonin na dubu dari a mako ga daidaikum al umma sai kuma dubu dari biyar ga kamfani a mako. Lamarin da baiyiwa al ummar kasar dadiba wanda hakan ya haifar da cece kuce a tsakanin al ummar kasar. To sai dai a yanzu Babban bankin ya janye aniyar tashi. Babban bankin yace kawo yanzu daidaikum jama a zasu iya cire dubu dari biyar a mako in kum ya zarce haka to za cajesu kaso uku cikin dari na abunda zasu cire maimakon kaso biyar wanda aka ayyana tun farko. A yayinda kamfanoni zasu iya cire milyon biyar a mako in ya zarce haka to suma za cajesu kaso biyar cikin dari na abinda zasu cire. Maimakon kaso goma da aka ayyana tun farko. Kuma wanan sabon dokan zaifara aikine daga ranan tara ga watan janairun shekara da dubu biyu da ashirinda uku.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE