Majalisar addinin musulunci a jahar ta gudanar da taron Da awa a karamar hukumar Gombi dàke jahar Adamawa.

Majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa ta kudiri aniyar hada kan musulmai dake fadin jahar ta Adamawa baki daya. Shugaban majalisar addinin misuluncin a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne ya tabbatar da haka a lokacinda yake jawabi a wurin taron Da awa wanda majalisar ta shiraya a yankin mazabar tsakiya jahar wanda aka gudanar a karamar hukumar Gombi dake jahar ta Adamawa. Alhaji Gambo Jika yace yanzu lokaci yayi da al ummah musulmai zasu kasance tsintsiya madaurinki daya ba tare da nuna banbancin a kidaba wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen samun cigaba addinin musuluncin yadda ya kamata. Don hakanema ya kirayi sarakunan gargajiya da sukasance masu basu hadin kai da goyon baya domin ganin sun kai ga nasara wajen hadin kai a tsakanin al ummah musulmai. Ya kuma kiaryi yan siyasa dasu kasance masu basu hadin kai wajen amsa gaiyyata da suke musu domin acewarsa indan suka gaiyaci yan siyasa a wurin tarurrukansu basa halrta illa kalilan daga cikinsu. Shima da yake gudanar da jawabinsa Hakimin Guyaku wato Gombi Alhaji Usman Ibrahim sarkin Fada ya jinjinawa majalisar addinin musulunci bisa wannan shirya taron Da awa wanda acewarsa hakan zai tamaka kwarai wayarwa al ummah musulmai kai dangane da muhimmancin hadin kai a tsakanin al ummah musulmai. Alhaji Usman ya shawatci majalisar addinin musulunci da ta maida hankalin kan fadakar da matasa dangane da sanin muhimmancin addinin musulunci dama hadin kai a tsakanin al ummah musulmai. Tunda farko a jawabin na maraba shugaban kwamitin Da awa na majalisar addinin musulunci wanda kuma shine mataimakin shugaban majalisar addinin musulunci na biyu a jahar Adamawa Modibbo Aliyu wuro Yamabe yace domin suga sunkai ga samun nasarane yasa suka hada kungiyoyin addinin musulunci daban daban wadanda ke fadin jahar baki daya. Ya kuma nuna jin dadinsa dangane da yadda jama a daga sassa daban daban suka halarci taron tare da yin fatan kowa ya kuma gidansa lafiya. Shikuwa shugaban karamara hukumar Gombi Alhaji Abdulraham Dauda Shaga shima nuna farin cikinsa yayi dangane da wannan taro tare da nuna goyon bayansa dari bisa dari domin ganin majalisar addinin musulunci ta cimma nasara na hadin kan al ummah musulmai baki daya. Suma a jawabainsu na fatan alheri wakilain kungiyoyon addinai daban daban da suka hada da na Izala mai shelkwata a Jos, da Izala na Kaduna, tare da kungiyar Jama atu Nasaril Islam da na Annahada, da Fityanul Islam. MSSN da muzaunamatu Islam da dai sauransu sun fatan ganin an cimma nasaran hadin kai a tsakanin tsakanin al ummah musulmai tare da yin adu ar neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen ganin an gudanar da Babbàn zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.