Manoma dake yankin baggare sun koka dangane da barnan da kwari ke kusu a ginakai.

Manoma a yankin baggare a cikin karamar hukimar yola ta kudu a jahar Adamawa sun baiyana cewa wasu kwari sun addabi gonakainsu wanda hakan ya sanyasu cikin rashin tabbas na gudanar da harkokin noma a yankin. Manoman sun baiyana hakane a zantawarsu da Jarida Al Nur dangane da halin da suke ciki na matsalat kwarin a gonakain nasu. Hassan Ali Soja manomine kuma shine Ardon Fulanin gwalamba kuma mataimakin shugaban kungiyar Tabbatil Pulaku Jamde Jam Foundation a jahar Adamawa. Yace sun rungimi harkan noman rani amman abunda yake ci musu tuwo a kwarya shie kwari domin suna cinye musu nau o in abundant suka shuka musamma masara. Don haka ya zama wajibi su kirayi gwamnatin jahar dana tarayya da su kawo musu daukin gaggawa domin ceto amfanin ganakain nasu. Mallam Shehu yace a gaskiya suna cikin wani yanayi na bukatar taimako ga wurin gwamnati saboda sun riga sunyi shuka kuma amfanin gona ya fita yadda ya kamata saidai kwari su addabesu sosai. Saboda suna bukatan a taimaka musu da magunguna domin magancce katsalar kwarin gaba daya. Shima anashi bangaren Kallam Zakar Ya u yace sukam basa ma samun tallafin da hwamnati ke baiwa manoma sai dai su ji a wani wuri saboda suna fatan wannan lokaci gwamnatin za ta tuna dasu ta kawo musu tallafi domin su bunkasa harkokin noma a yankin nasu yadda ya kamata.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE