Makarantar gwamnati GSS Numan tayi nasara akan takwaranta na kamfanin Dangode.

Makarantar gwamnati wato GSS Numan ta yi nasarar doke makarantan kamfanin dangote a wani gasar kwallon kafa da aka gudanar a garin numan. Kamfanin Dangote ne ya shirya Gasar kwallon kafar, da zimmar gina kyakkyawar mu’amala tare da gina harkokin wasanni na matasa dake garuruwa dake kewaye da shi. Da yayi jawabi a ranar kammala gasar, shugaban kamfanin Dangote dake Numan, Mista Chinanya Silvail, wanda ya samu wakilcin shugaban sashin ci gaban filaye na kamfanin, Ibrahim Mohammed Doka yace makasudin shirya wannan gasa shi ne domin hada kan al’umma dake kewaya da kamfanin. A cewar shi, wannan ne karo na farko da kamfanin Dangote ke shirya irin wannan gasa na kwallon kafa, kuma zai ci gaba da shirye ire iren wadannan gasa cikin jerin aiyuka da yake gudanarwa. Hakimin garin borrong, cif Lwassam Gadddiel Naina wanda ya wakilci masarautan kasar Mbula a bukin rufe gasar, ya yabawa kamfanin suga na Dangote dashirya wa matasan yankin wannan gasa, tare da kira ga sauran kungiyoyi da su yi koyi. Tun farko dai a jawabin shin a maraba, shugaban karamar hukumar Numan, Christopher Sofore, ya mika godiya wa kamfanin suga na Dangote dake Numan da wannan kokari na shirya irin wannan gasa. Sofore ya kirayi yan wasan dasu sa himma tare da kiyayewa yayin karawa da zasuyi, tare da Karin cewa babu wanda aka doke domin manufar shirya gasar shine samun hadin kai kuma anyi nasarar cin ma hakan. Gasar kwallon kafar na tsawon mako guda an kammala shi ne a ranar asabar, sha bakwai ga watan disamban 2022 tare da halattar kungiyoyin taka leda na makarantun sakandare da suka wakilci kananan hukumomin Numan, Demsa, Lamurde, Guyuk , Shelleng , da kuma makarantan kamfanin dangote wato DSR High school. Makarantan gwamnati na GSS Numan ta doke makarantan sakandaren dangote bayan bugun daga kai sai mai tsaron raga, tare da cin kambun zinari a gasar da kyautan kudi naira dubu dari biyu. Makarantan sakandare na Dangote da ta zo na biyu ta samu azurfa da kyautan kudi naira dubu dari da hamsin, sai makarantan GSS Lamurde da ta zo na uku, ta kuma samu tagulla da kyautan kudi naira du bu dari. Wasu Karin wadanda aka baiwa kyaututtuka sun hada da na dan wasa da fi taka leda, sai mai tsaron raga da yayi fice da dai sauran su.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE