Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta ceto mutene hudu tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane a tsaunin dutsen mboi dake cikin karamar hukumar Song a jahar Adamawa.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran ceto mutane hudu tare da tarwatsa maboyar yan ta adda da suka addabi yankin mboi dake ciki karamar hukumar Song a jahar Adamawa.
Kakain rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanar da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan tace rundunan ta gano wayoyin hanu, sarka, bargo, da dai sauransu, a maboyar bata garin a tsaunin dutsen mboi dake cikin karamar hukumar ta Song a jahar Adamawa.
Sanarwa tacigaba da cewa ofishin yan sandan dake gundumar Song tare da hadin gwiwar mafarauta ne aka samu nasaran tarwatsa gungun yan ta addan.
Kuma an dauki matakin haka ne biyo bayan rahoton da ake samu na ywan sace sacen shanu, garkuwa da mutane, fashi da makami, wanda hakan yasa Jami an yan sandan yin arangama da wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne wanda kuma sun gudu da raunin harbin bindiga a jikinsu.
Kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa Sikiru Kayode Akande ya yabawa DPO dake kula da ofinshin yan sandan dake Song, da jaimi ansa tare kuma da mafarauta bisa wannan na mijin kokari da sukayi na dakile aiyukan masu sikata laifuka a yankin.
Kwamishinan ya kuma kirayi al ummar jahar Adamawa da su kasance masu taimakawa rundunan yan sandan hadin kai da goyon baya domin ganin rundunan ta samu nasaran kare rayuka dama dukiyoyin Al umma baki daya.
Comments
Post a Comment