Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta fatattaki wadanda ake zargi masu garkuwa da mutanene.
A kokarinta na dakile aiyukan da addanci a jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar ta Adamawa tayi nasaran tarwatsa wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne a cikin karamar hukumar Gombi dake jahar Adamawa.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan tace an samu nasaran haka ne biyo bayan bayanai da aka samu cewa wasu mutane da basu wuce biyarba dauke da makamai inda suka kaiwa wani mai suna Musa Muhammed hari wanda a yanzu hakama yana jinya a asibiti sakamokon raunuka da ya samu biyo bayan harinda mutanen suka kai masa.
Daga jin bayanin haka ne rundunan batayi da wasaba inda suka halarci inda lamarin ya faru karkaahin jagirancin D P O dake kula da ofishin yan sandan dake karamar hukumar Gombi. Tare da hadin gwiwar mafarauta suka kai dauki inda sukabi kafan wadanda ake zargi da kai harin wanda kuma akayi nasara tarwatsasu tare da hallaka mutane biyu da kuma gano bindiga kiran Ak 47 guda daya.a yayin da sauran sun arce da raunin harbi a jikinsu.
Don haka nema kwamishinan yan sandan Jahar Adamawa CP Sikiru Kayode Aknde ya yabawa D P O Gombi da Jami ansa da kuma mafarauta bisa wannan na mijin kokari da sukayi. Tare da kiran daukacin al umma jahar Adamawa da su cigaba da taimakawa rundunan yan sandan da wasu bayanai da zai baiwa rundunar dama dakile aiyukan bata gari a tsakanin al umma.
Kwamishinan ya kuma tabbatarwa al umma jahar ta Adamawa cewa rundunan a shirye take wajen kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya.
Comments
Post a Comment