Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin ganin an kammala bukukiwar kirsemeti dama sabuwar shekara lafiya.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta baza komarta a dukkanin kanaan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar domin ganin an yi bukukuwar kirisemeti dama sabuwar shekara lafiya ba tare davhatsaniyaba. Rundunan ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin rundunan SP Suleiman Yahaya Ngurije ya sanyawa hanu wanda aka rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. A cikin sanarwan an jiyo kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa C P Sikiru Kayode Akande na umurtan dukkanin Jami an yan sandan dake yankuna harms dana kananan hukumomi da su daura damaran ganin sun saka kafar wanda daya ga duk wanda zaiyiwa doka karan tsaye tare da tabbatar da ganin an kare rayuka dama dukiyoyin al umma a lokaci dama bayan bukukuwar kirisemeti har da sabuwar shekara. Kwamishinan yace tunin rundunan ta kimtsa tsaf domin tura Jami anta a wuraren ibada dama wuraren tarurruka dake fadin jahar. Don haka nema yake tabbatarwa al ummar jahar da sugudanar da lamaransu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargababa. Saboda haka kwamishinan ya kirayi daukacin al ummar jahar da su kasance masu taimakawa rundunan yan sandan da wasu bayanain sirri wanda hakan zai baiwa rundunan damar dakile aiyukan bata gari a tsakanin al ummar. Kwamishinan yan sandan ya kuma taya gwamnatin jahar Adamawa karkashin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri dama al ummar jahar murnan bikin kirisemeti da ma sabuwar shekara. Dafatan za a kammala bukukuwar lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE