Wasu Mazauna Jalingo sun kirayi hukumar zabe da ta samar musu da katin zabe kafin ranan Babban zabe.
Wasu mazauna Cikin grain Jalingo fadar gwamanatin jahar Taraba musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe,kuma ba su samu katinsuba. sun kirayi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC shiyar jahar Taraba da ta samar musu da katin kafin ranan Babban zabe.
Sunyi wannan kirane a lokacinda suka zanta da manema labarai a dai dai lokacin da sukaje karban katinsu amma ba suga nasuba wanda kuma hukumar zabe ta fara rarraba katin zaben ne daga ranan 12-12-2022.
Wadanda basu katin nasuba sun baiayana shelkwatan hukumar ne to amma sai akace nasu bai fitoba tukunna, saboda haka su sake dawowa.
Daya daga cikin mazauna garin na jalingo mai suna Victoria Baraya tace ta kasance a ofishin hukumar ne domin karban katin ta amma sai aka shaidamata cewa ta dawo ran 6-1-2023. tace kokadan bataji dadiba saboda tanaso tayi amfanin dashi kafin ranan zabe.
Wani kuma mai suna Baahir Abba shima ya baiyana rashin jindadinsa da akece nashi katin bai fitoba ahima ancemasa ya da wo a watan janairu domin karban nasa katin kuma ya ga mutane da dama suna karban nasu katin.
Wadanda suka karbi nasu katin irinsu Grace Ishaku, Jonathan Joel, Babangida Musa, da kuma Zara Usman sunce rarraba katin yana tafiya dai dai.
Shugabar sashin ilimartawa da watsa labarain hukumar aJalingo Mrs Rachel Ngunan Iyongo tace rarraba katin yana tafiya ba tare da matsalaba. Tare da cewa Jami an hukumar dake rarraba katin suna aikine daga ranan litinin zuwa lahadi, don haka nema ta shawarci wadanda katin su ya fita da suzo sukarbi katinsu.
Ta kuma tabbatarwa al umma jahar musammanma wadanda sukayi rijistan katin zabe zasu samu katin zabensu kafin ranan Babban zaben shekara ta 2023.
Comments
Post a Comment