Yan takaran gwamnoni sun sanya hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya a jahar Adamawa.

An ja hankalin yan takaran kujeran gwamna dake jahar Adamawa da su tabbatar da aiwatar da zaben 2023 cikin zaman lafiya. Kwamishina hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, na jahar Adamawa, Hudu Yunusa Ari ne ya yi wannan jan hankali yayan zaman rattaba hannu da yan yakaran suka yi na yarjejeniyar zaman lafiya yayin gudanar da harkokin siyasa a Jihar. An dai gudanar da taron sanya haunne a otel na Madugu Rockview, dake nan yola.wanda kuma an yi hakan ne domin samun tabbacin aiwatar da zaben gwamnan jahar da ke tafe a shekara ta 2023 cikin zaman lafiya. Kwamishnan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, na jahar Adamawa, Hudu Yunusa Ari yace a ko da yaushe tashe tashen hankali na yi wa harkokin aiwatar da zabuka masu inganci barazana, shi yasa ake bukatan yan takaran su ba da tabbacin samun zaman lafiya ta hanyar rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar zaman lafiya. Hudu ya kuma bukace yan takaran da kowa ya nuna amincewar shi ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyan, wanda hakan zai nuna cewa za su gina harkokin neman kuri’un su kan batutuwam ci gaba. Ya kuma shaida musu cewa itama hukumar zabe mai zaman kanta zata aiwatar da sahihin zabe. A na shi jawabi, kwamishinan yan sandan jahar Adamawa, wanda shine shugaban komitin tuntuba kan harkokin tsaro na zabuka dake jahar, CP Sikiru Akande yace, jahar Adamawa ta tabbatar da mishi irin matakin zaman lafiya da take da shi a zabuka da akayi a can baya, wanda ya alakanta da irin yan takara da suka amince domin tabbatar da gudanar da zabe cikin zaman lafiya yayin tafiyar da harkokin zabukan. Ya kuma bada tabbacin cewa, jami’an ysaro dake jahar zasu samar da kyakkyawar yanayin tsaro wa dukkan yan siyasa ba tare da la’akari da jam’iya da suka fito ba. Da suka baiyana yakinin su kan wannan rattaba hannun yarjejeniyar zaman lafiya, wasu daga cikin yan takara da suka kasance a zaman sun shaida wa manema labarai cewa, shakka babu hakan zai taimaka wajen tabbayar wa al’umma zabin su. Yan takara goma daga cikin goma sha sha biyar da ake sa ran zasu hallaci zaman ne su ka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyan a gaban shugabannnin gargajiya, shugabannin cibiyoyin tsaro da ma wasu masu ruwa da tsaki da suka hallaci zaman.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.